‏ Exodus 37:17-24

Wurin ajiye fitila

(Fitowa 25.31-40)

17Suka yi wurin ajiye fitila da zinariya zalla, suka yi gindinsa da kuma gorar jikinsa, da ƙerarriyar zinariya. Kwaf wurin ajiye fitila da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da wurin ajiye fitilan. 18Akwai rassa guda shida da suka miƙe daga gefe wurin ajiyar fitilar, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan. 19A reshe guda na wurin ajiye fitilan, akwai kwaf uku masu kama da tohon almon, akwai kuma uku a reshe na biye, haka kuma suke a dukan rassa shida da suke daga wurin ajiye fitilan. 20A bisa wurin ajiye fitilan kuma akwai kwaf huɗu da aka yi su kamar furannin almon da toho da kuma mahaɗai. 21Toho ɗaya yana a ƙarƙashin rassa biyu waɗanda suke daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu yana a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku kuma yana a ƙarƙashin rassa biyu na uku, duka-duka rassa shida ne. 22An ƙera mahaɗai da rassa wurin ajiye fitila a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi wurin ajiye fitilar da dukan komensa a haɗe.

23Da zinariya zalla suka yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa. 24Daga talenti ɗaya na zinariya zalla suka yi wurin ajiye fitila da dukan kayayyakinsa.
Copyright information for HauSRK