Exodus 38:1-7
Bagaden hadaya ta ƙonawa
(Fitowa 27.1-8)
1Suka gina bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba’i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku. 2Suka yi ƙahoni a kusurwansa huɗu, ƙahonin da bagade a haɗe suke, suka kuma dalaye bagaden da tagulla. 3Da tagulla kuma ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta. 4Suka yi wa bagaden raga, tagulla kuma don yă sa shi a tsakiya. 5Suka yi zubin zoban tagulla don riƙe sanduna a kusurwoyi huɗu na ragar tagullar. 6Suka yi sanduna da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da tagulla. 7Suka sa sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefen bagade don ɗaukarsa, suka yi rami cikinsa.
Copyright information for
HauSRK