‏ Exodus 40:34-38

Ɗaukakar Ubangiji

34Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji ta cika tabanakul. 35Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika tabanakul.

36Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul. 37Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi. 38Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.
Copyright information for HauSRK