‏ Ezekiel 3:16-21

Kashedi ga Isra’ila

(Ezekiyel 33.1-9)

16A ƙarshen kwana bakwai ɗin maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 17“Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro don gidan Isra’ila; saboda haka ka ji maganar da zan yi ka kuma yi musu kashedin nan da ya fito daga gare ni. 18In na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ ba ka kuwa yi masa kashedi ko ka tsawata masa a kan mugayen hanyoyinsa don yă ceci ransa ba, wannan mugun zai mutu saboda
Ko kuwa cikin; haka ma a ayoyi 19 da kuma 20
zunubinsa, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka.
19Amma in ka yi wa mugun kashedi bai kuwa juya daga mugayen hanyoyinsa ba, zai mutu saboda zunubinsa; amma kai kam za ka kuɓuta.

20“Har yanzu, in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya aikata mugunta, na kuma sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Da yake ba ka yi masa kashedi ba, zai mutu saboda zunubinsa. Ba za a tuna da abin adalcin da ya yi ba, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka. 21Amma in ka yi wa mai adalcin kashedi kada yă yi zunubi bai kuwa yi zunubi ba, tabbatacce zai rayu saboda ya ji kashedin, kuma kai kam za ka kuɓuta.”
Copyright information for HauSRK