Ezekiel 33:1-9
Ezekiyel mai tsaro
(Ezekiyel 3.16-21)
1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2“Ɗan mutum, yi magana da mutanen ƙasarka ka faɗa musu cewa, ‘Sa’ad da na kawo takobi a kan ƙasar, mutanen ƙasar kuwa suka zaɓi ɗaya daga cikin mutanensu suka mai da shi mai tsaro, 3ya kuma ga takobi yana zuwa a kan ƙasar ya kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane, 4in wani ya ji busar amma bai kula ba, takobin zai zo ya ɗauki ransa, jininsa kuwa zai zauna a kansa. 5Da yake ya ji ƙarar busar amma bai kula ba, jininsa zai zauna a kansa. Da a ce ya kula, da ya ceci kansa. 6Amma a ce mai tsaron ya ga takobi yana zuwa bai kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane ba sai takobi ya zo ya ɗauki ran waninsu, za a kawar da wannan mutum saboda zunubinsa, amma zan nemi hakkin jinin mutumin a kan mai tsaron.’ 7“Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro bisa gidan Isra’ila; saboda haka ka ji abin da zan faɗa ka kuma gargaɗe su. 8Sa’ad da na ce wa mugu, ‘Ya mugun mutum, tabbatacce za ka mutu,’ kai kuma ba ka yi magana don ka juyar da shi daga hanyoyinsa ba, wannan mugun mutum zai mutu ▼▼Ko kuwa ciki; haka ma a aya 9
domin zunubinsa, zan kuma nemi hakkin jininsa a kanka. 9Amma in ka faɗakar da mugun mutumin don yă juye daga hanyoyinsa bai kuwa yi haka ba, zai mutu saboda zunubinsa, amma kai za ka kuɓutar da kanka.
Copyright information for
HauSRK