‏ Genesis 11:10-26

Daga Shem zuwa Abram

10Wannan shi ne labarin Shem.

Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad.
11Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
12Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela. 13Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
Da Ibraniyanci; Seftuwajin (dubi kuma Luk 3.35,36 da kuma sharhi a Far 10.24) shekaru 35, ya haifi Kainan. 13 bayan kuma ya haifi Kaina, Arfakshad ya yi shekaru 430 ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata, sa’an nan ya mutu. Sa’ad da Kaina ya yi shekaru ɗari da talatin, ya haifi Shela. Bayan ya haifi Shela, Kaina ya yi shekaru 330 ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata

14Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber. 15Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
16Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg. 17Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
18Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu. 19Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
20Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug. 21Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
22Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor. 23Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
24Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera. 25Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
26Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.
Copyright information for HauSRK