Genesis 25:1-4
Mutuwar Ibrahim
1Ibrahim ya auro wata mace, mai suna Ketura. 2Ta haifa masa Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. 3Yokshan shi ne mahaifin Sheba da Dedan. Zuriyar Dedan su ne mutanen Ashur, da mutanen Letush, da kuma mutanen Lewummin. 4’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida, da kuma Elda’a. Dukan waɗannan zuriyar Ketura ce.
Copyright information for
HauSRK