‏ Genesis 36:1-14

Zuriyar Isuwa

1Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).

2Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye 3ya kuma auri Basemat’yar Ishmayel wadda take’yar’uwar Nebayiwot.

4Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel. 5Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.

6Isuwa ya ɗauki matansa da’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub. 7Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu. 8Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.

9Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir.

10Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Isuwa maza,
Elifaz, ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.
11’Ya’yan Elifaz maza su ne,
Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.
12Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.
13’Ya’yan Reyuwel maza su ne,
Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
14’Ya’yan Oholibama maza’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne,
Yewush, Yalam da Kora.
Copyright information for HauSRK