Genesis 36:20-43
20Waɗannan su ne’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin,Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, 21Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa,’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
22’Ya’yan Lotan maza su ne,
Hori da Homam. ▼
▼Da Ibraniyanci Hemam, wani suna na Homam (dubi 1Tar 1.39)
Timna’yar’uwar Lotan ce.23’Ya’yan Shobal maza su ne,
Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.
24’Ya’yan Zibeyon maza su ne,
Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ▼
▼Bulget, Siriyak sami ruwa; ma’anar Ibraniyanci don wannan kalma ba tabbatacce ba ne.
ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.25’Ya’yan Ana su ne,
Dishon da Oholibama’yar Ana.
26’Ya’yan Dishon maza ▼
▼Da Ibraniyanci Dishan, wani suna na Dishon
su ne,Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
27’Ya’yan Ezer maza su ne,
Bilhan, Za’aban da Akan.
28’Ya’yan Dishan maza su ne,
Uz da Aran.
29Waɗannan su ne manyan Horiyawa,
Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, 30Dishon, Ezer da Dishan.
Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.
Masu mulkin Edom
31Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki, ▼▼Ko kuwa kafin wani sarkin Isra’ilawa ya yi mulki a kansu
32Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.
33Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi.
34Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.
35Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit.
36Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.
37Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi ▼
▼Mai yiwuwa Yuferites
ya gāje shi.38Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi.
39Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ▼
▼Yawancin rubuce-rubucen hannu na Masoretik, Fentatut na Samariya da Siriyak (dubi kuma 1Tar 1.50); yawancin rubuce-rubucen hannu na Masoretik suna da Hadar ne.
ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.40Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne,
Timna, Alwa, Yetet.
41Oholibama, Ela, Finon.
42Kenaz, Teman, Mibzar.
43Magdiyel da Iram.
Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna.
Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.
Copyright information for
HauSRK