‏ Isaiah 37:21-35

Fāɗuwar Sennakerib

(2 Sarakuna 19.20-34)

21Sa’an nan Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo wa Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa. Saboda ka yi addu’a gare ni game da Sennakerib sarkin Assuriya, 22ga abin da maganar Ubangiji ya faɗa a kansa, “Budurwa Diyar Sihiyona
ta rena tana kuma maka ba’a.
Diyar Urushalima
tana kada kai yayinda kake gudu.
23Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo?
A kan wa ka tā da muryarka
ka kuma daga idanu cikin fariya?
A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila!
24Ta wurin jakadunka
ka jibge zage-zage a kan Ubangiji.
Ka kuma ce,
‘Da kekunan yaƙina masu yawa
na hau ƙwanƙolin duwatsu,
ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon.
Na sassare al’ul mafi tsayi
fir mafi kyau.
Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.
25Na haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa
na kuma sha ruwa a can.
Da tafin ƙafafuna
na busar da dukan rafuffukan Masar.’

26“Ba ka ji ba cewa
tun dā can na shirya ya zama haka?
A kwanakin dā na kafa shi;
yanzu na sa ya faru,
cewa ka mai da birane masu mafaka
zuwa tsibin ɓuraguzai.
27Mutanensu, suka rasa ƙarfi,
sun firgita suka kuma sha kunya.
Suka zama kamar tsire-tsire a gona,
kamar tsire-tsiren ta suka tohu,
kamar ciyawar da ya tsiro a kan rufi,
wadda zafi ya yi wa ƙuna kafin tă yi girma.

28“Amma na san inda kake zama
da sa’ad da kakan fita ka kuma koma
da yadda ka harzuƙa gāba da ni.
29Saboda ka harzuƙa gāba da ni
kuma saboda girmankanka ya kai kunnuwana,
zan sa ƙugiya a hancinka
linzamina a bakinka,
zan kuma sa ka koma
ta hanyar da ka zo.

30“Wannan zai zama alama gare ka, ya Hezekiya, “Wannan shekara za ka ci abin da ya yi girma da kansa,
shekara ta biyu kuma abin da ya tsiro daga wancan.
Amma a shekara ta uku za ka yi shuki ka kuma girba,
za ka dasa gonakin inabi ka kuma ci’ya’yansu.
31Sauran da suka rage na gidan Yahuda kuwa
za su yi saiwa a ƙarƙashi su kuma ba da’ya’ya a bisa.
32Gama daga Urushalima raguwa za tă fito,
kuma daga Dutsen Sihiyona ƙungiyar waɗanda suka tsira.
Himmar Ubangiji Maɗaukaki
zai cika wannan.

33“Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga wannan birni ba
ya harbe kibiya a nan.
Ba zai zo gabansa da garkuwa ba
ko ya gina mahaurai kewaye a kansa ba.
34Ta hanyar da ya zo da ita zai koma;
ba zai shiga wannan birni ba,”
in ji Ubangiji.
35“Zan kāre wannan birni in kuma cece shi,
saboda girmana da kuma saboda sunan Dawuda bawana!”
Copyright information for HauSRK