‏ Jeremiah 10:12-16

12Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa;
ya kafa duniya ta wurin hikimarsa
ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
13Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi;
yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya.
Yakan aiki walƙiya da ruwan sama
ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa.

14Kowa marar azanci ne, marar ilimi;
kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa.
Siffofinsa ƙarya ne;
ba su da numfashi a cikinsu.
15Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne;
Sa’ad da hukuncinsu ya yi za su lalace.
16Shi da yake Rabon Yaƙub ba kamar waɗannan yake ba,
gama shi ne Mahaliccin abubuwa duka,
har da Isra’ila, kabilar gādonsa
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
Copyright information for HauSRK