Jeremiah 52:1-3
Fāɗuwar Urushalima
(2 Sarakuna 24.18–25.30; 2 Tarihi 36.11-21)
1Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal,’yar Irmiya, wanda yake zaune a Libna. 2Sarki Zedekiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehohiyakim ya yi. 3Al’amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra’ila da Yahuda, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala. Zedekiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babilon.
Copyright information for
HauSRK