‏ Jeremiah 7:1-15

Banzancin addinin ƙarya

(Irmiya 26.1-6)

1Maganar da ta zo wa Irmiya ke nan daga Ubangiji. 2“Ka tsaya a ƙofar gidan Ubangiji, a can kuwa ka yi shelar wannan saƙo.

“ ‘Ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi don yin sujada ga Ubangiji.
3Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allahna Isra’ila, yana cewa ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, zan kuwa bar ku ku zauna a wannan wuri. 4Kada ku dogara ga maganganun nan na ruɗarwa cewa, “Wannan shi ne haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji!” 5In dai kuka canja hanyoyinku da ayyukanku kuma kuna aikata adalci da junanku, 6in ba ku zalunci baƙo, maraya ko gwauruwa ba kuma in ba ku zub da jinin marar laifi a wannan wuri ba, in kuma ba ku bi waɗansu alloli da za su cuce ku ba, 7to, zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasar da na ba kakanninku har abada abadin. 8Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani.

9“ ‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba, 10sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama? 11Wannan gidan da ake kira da Sunana ya zama kogon’yan fashi ne a gare ku? Amma ina kallo! In ji Ubangiji.

12“ ‘Yanzu ku fita zuwa Shilo inda na fara maishe shi wurin zama don Sunana, ku ga abin da na yi masa saboda muguntar mutanen Isra’ila. 13Yayinda kuke yin dukan waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji, na yi muku magana sau da sau, amma ba ku ji ba; na kira ku, amma ba ku amsa ba. 14Saboda haka, abin da na yi wa Shilo shi ne yanzu zan yi wa gidan da ake kira da Sunana, haikalin da kuka dogara a kai, wurin da na ba ku da kuma kakanninku. 15Zan kore ku daga gabana, kamar yadda na yi ga dukan’yan’uwanku, mutanen Efraim.’
Copyright information for HauSRK