‏ John 11:45-53

An ƙulla shawara a kashe Yesu

(Mattiyu 26.1-5; Markus 14.1,2; Luka 22.1,2)

45Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi. 46Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa.

Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa.
48In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.”

49Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba! 50Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”

51Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa, 52ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya. 53Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa.
Copyright information for HauSRK