John 12:12-19
Shiga mai nasara
(Mattiyu 21.1-11; Markus 11.1-11; Luka 19.28-40)
12Kashegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima. 13Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa, “Hosanna!”“Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” ▼
▼Zab 118.25,26
“Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!”
14Yesu ya sami ɗan jaki, ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa, 15“Kada ki ji tsoro, ya Diyar Sihiyona;
duba, ga sarkinki yana zuwa,
zaune a kan aholaki jaki.” ▼
▼Zak 9.9
16Da fari almajiransa ba su gane dukan wannan ba. Sai bayan da aka ɗaukaka Yesu, sa’an nan suka gane cewa an rubuta waɗannan abubuwa game da shi ne, har ma suka yi masa waɗannan abubuwa. 17Taron da suke tare da shi a sa’ad da ya kira Lazarus daga kabari ya kuma tā da shi daga matattu suka yi ta baza labarin. 18Mutane da yawa kuwa suka fita taryensa, saboda sun ji labarin abin banmamakin da ya yi. 19Saboda haka Farisiyawa suka ce wa juna, “Duba, wannan ba ya kai mu ko’ina. Ga shi, duk duniya tana bin sa!”
Copyright information for
HauSRK