‏ John 13:36-38

(Mattiyu 26.31-35; Markus 14.27-31; Luka 22.31-34)

36Siman Bitrus ya tambaye shi ya ce, “Ubangiji ina za ka?”

Yesu ya amsa ya ce, “Wurin da za ni, ba za ka iya zuwa yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.”

37Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan binka yanzu ba? Zan ba da raina saboda kai.”

38Sai Yesu ya amsa ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku!
Copyright information for HauSRK