John 18:19-24
Babban firist ya yi wa Yesu tambayoyi
(Mattiyu 26.59-66; Markus 14.55-64; Luka 22.66-71)
19Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa. 20Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majami’u ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba. 21Don me kake tuhumata? Ka tambayi waɗanda suka ji ni. Ba shakka, sun san abin da na faɗa.” 22Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin ma’aikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?” 23Yesu ya amsa ya ce, “In na faɗi abin da ba daidai ba, ka nuna abin da ba daidai ba. Amma in gaskiya na faɗa, don me ka mare ni?” 24Sai Annas ya aika da shi, a daure, wurin Kayifas babban firist.
Copyright information for
HauSRK