John 18:3-11
3Saboda haka Yahuda ya zo cikin lambun, yana jagoranta ƙungiyar sojoji da waɗansu ma’aikata daga wurin manyan firistoci da Farisiyawa. Suna riƙe da toci, fitilu da kuma makamai. 4Yesu kuwa, sane da duk abin da zai same shi, ya fito ya tambaye, su ya ce, “Wa kuke nema?” 5Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce, “Ni ne shi.” (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.) 6Da Yesu ya ce, “Ni ne shi,” sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa. 7Sai ya sāke tambayar su ya ce, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.” 8Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku ni ne shi. In kuma ni ne kuke nema, to, sai ku bar waɗannan su tafi.” 9Wannan ya faru ne don a cika kalmomin da ya yi cewa, “Ban yar da ko ɗaya daga cikin waɗanda ka ba ni ba.” ▼▼Yoh 6.39
10Sai Siman Bitrus, wanda yake da takobi, ya zāre, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama (Sunan bawan kuwa Malkus ne.) 11Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?”
Copyright information for
HauSRK