‏ Leviticus 23:4-8

Bikin Ƙetarewa da Burodi Marar Yisti

(Ƙidaya 28.16-25)

4“ ‘Waɗannan su ne bukukkuwan da Ubangiji ya kafa da tsarkakakkun taron jama’a za su yi a ƙayyadaddun lokuta. 5Bikin Ƙetarewar Ubangiji, zai fara da yamma a ranar goma sha huɗu na wata na fari. 6A rana ta goma sha biyar na wannan wata, za a fara Bikin Burodi Marar Yisti na Ubangiji. Za ku yi kwana bakwai kuna cin burodi marar yisti. 7A rana ta fari, ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba. 8Kwana bakwai za ku miƙa hadaya ga Ubangiji da wuta. A rana ta bakwai ɗin ku yi taro mai tsarki, ba za ku kuwa yi aiki na kullum ba.’ ”
Copyright information for HauSRK