Leviticus 26:3-13
3“ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina, 4zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu’ya’yansu. 5Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku. 6“ ‘Zan ba ku salama a ƙasar, za ku kuwa kwanta, kuma babu wani da zai tsorata ku. Zan kori mugayen namun jeji daga ƙasar, takobi kuma ba zai ratsa cikin ƙasarku ba. 7Za ku kori abokan gābanku, za su kuwa fāɗi a kaifin takobi a gabanku. 8Mutanenku biyar za su kori mutum ɗari, mutanenku ɗari kuma za su kori mutane dubu goma, abokan gābanku kuma za su fāɗi a kaifin takobi a gabanku. 9“ ‘Zan dube ku da idon rahama, in kuma sa ku riɓaɓɓanya ku kuma ƙaru, zan kiyaye alkawarina da ku. 10Za ku ci gaba da cin girbin bara, har ku fitar da shi don ku sami wurin saboda sabo. 11Zan kafa wurin zamana a cikinku, ba zan kuma yi ƙyamarku ba. 12Zan yi tafiya a cikinki in kuma zama Allahnku, za ku kuwa zama mutanena. 13Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar don kada ku ƙara zama bayi ga Masarawa; na karya sandunan wahalarku, na kuma bar ku ku yi tafiya a sake.
Copyright information for
HauSRK