Luke 11:29-32
Alamar Yunana
(Mattiyu 12.38-42; Markus 8.12)
29Da taron mutane suka ƙaru, sai Yesu ya ce, “Wannan mugun zamani ne. Tana neman wani abin banmamaki, amma ba ko ɗaya da za a ba ta, sai dai ta Yunana. 30Kamar yadda Yunana ya zama alama ga mutanen Ninebe, haka ma Ɗan Mutum zai zama ga zamanin nan. 31A ranar shari’a, Sarauniyar Kudu za tă tashi tsaye tare da wannan zamani, ta yanke wa wannan zamani hukunci, domin ta zo daga ƙarshen duniya ta saurari hikimar Solomon, ga shi kuwa, shi wanda ya fi Solomon girma, na nan. 32A ranar shari’a, mutanen Ninebe za su tashi tsaye tare da wannan zamani, su yanke wa wannan zamani hukunci. Gama sun tuba sa’ad da Yunana ya yi musu wa’azi. Ga shi yanzu, shi wanda ya fi Yunana girma, na nan.
Copyright information for
HauSRK