Luke 11:34-36
34Idonka shi ne fitilar jikinka. Sa’ad da idanunka suna da lafiya, dukan jikinka ma na cike da haske, amma sa’ad da idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma na cike da duhu. 35Ka lura fa, kada hasken da yake cikinka ya zamana duhu ne. 36Saboda haka, in dukan jikinka yana cike da haske, ba inda ke da duhu, jikinka kuwa zai kasance da haske gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila yake haskaka ka.”
Copyright information for
HauSRK