‏ Luke 12:35-48

Zama a faɗake

(Mattiyu 24.45-51)

35 “Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci, 36kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan. 37Zai zama da albarka in maigida ya dawo, ya tarar da bayinsa suna zaman tsaro. Gaskiya ni faɗa muku, zai sa kayan hidima da kansa, ya sa bayinsa su zauna kan tebur, sa’an nan ya yi musu hidimar abinci. 38Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a sa’a ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne. 39Amma ku fahimci wannan. Da maigida ya san sa’ar da ɓarawo zai zo, ai, da ba zai bari a shiga, a fasa masa gida ba. 40Ku ma, sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku yi tsammani ba.”

41Bitrus ya yi tambaya ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa ga kowa da kowa ne?”

42Ubangiji ya amsa ya ce, “To, wane ne manaja mai aminci da hikima, wanda maigida ya ba shi riƙon bayinsa, domin ya ba su abincinsu a daidai lokaci? 43Zai zama da albarka ga bawan nan wanda maigidan ya dawo, ya same shi yana yin haka. 44Gaskiya nake gaya muku, maigidan zai ba shi riƙon dukan dukiyarsa. 45Amma da a ce bawan ya yi tunani a zuciyarsa ya ce, ‘Ai, maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ sa’an nan ya fara dūkan bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci, da sha, har da buguwa. 46Maigidan bawan nan zai dawo a ranar da wannan bawan bai yi tsammaninsa ba, kuma a sa’ar da bai sani ba. Maigidan zai yayyanka shi, ya kuma ba shi rabonsa tare da marasa bangaskiya.

47 “Bawan da ya san nufin maigidansa, kuma bai yi shiri ba, ko kuma bai yi abin da maigidansa yake so ba, zai sha mummunan duka. 48Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi.
Copyright information for HauSRK