‏ Luke 14:15-24

Misalin babban biki

(Mattiyu 23.37-39)

15Da jin haka, sai wani da yake tare da shi a tebur ɗin, ya ce wa Yesu, “Mai albarka ne wanda zai ci abinci a bikin nan a mulkin Allah.”

16Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa. 17Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa ya je ya ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, don an shirya kome.’

18 “Amma sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farkon ya ce, ‘Na sayi gona yanzun nan, dole in je in ga yadda take, ina roƙonka ka yi mini haƙuri.’

19 “Wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma yanzun nan, ina kan hanyata ke nan in gwada su, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’

20 “Har yanzu wani ya ce, ‘Na yi aure yanzun nan, don haka ni ba zan iya zuwa ba.’

21 “Bawansa ya dawo ya gaya wa maigidansa wannan. Sai maigidan ya yi fushi, ya ba da umarni ga bawansa ya ce, ‘Ka fita da sauri, ka bi titi-titi da lungu-lungu na garin, ka kawo matalauta, da guragu, da makafi, da shanyayyu.’

22 “Bawan ya dawo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, an yi abin da ka umarta, amma har yanzu da sauran wuri.’

23 “Maigidan ya ce wa bawansa, ‘Ka je kan hanyoyin da layi-layi na karkara, ka sa su shigo, don gidana ya cika.’ 24Ina gaya muku, babu ko ɗaya daga cikin mutanen nan da aka gayyata da zai ɗanɗana bikina.”
Copyright information for HauSRK