Luke 18:18-30
Mai mulki mai arziki
(Mattiyu 19.16-30; Markus 10.17-31)
18Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?” 19Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. 20Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ” 21Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.” 22Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.” 23Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai. 24Yesu ya kalle shi ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah! 25Tabbatacce, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.” 26Waɗanda suka ji wannan suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai iya samun ceto?” 27Yesu ya amsa ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.” 28Sai Bitrus ya ce, masa, “To, ga shi mun bar kome da muke da shi, don mu bi ka!” 29Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko’yan’uwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah, 30da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.”
Copyright information for
HauSRK