Luke 18:31-34
Yesu ya sāke magana a kan mutuwarsa
(Mattiyu 20.17-19; Markus 10.32-34)
31Sai ya kai Sha Biyun gefe ɗaya, ya ce musu, “Za mu Urushalima, kuma dukan abin da annabawa suka rubuta a kan Ɗan Mutum zai cika. 32Za a ba da shi ga Al’ummai, za su yi masa ba’a, su zage shi, su tofa masa miyau, 33za su yi masa bulala, su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma zai tashi.” 34Almajiran ba su gane da ko ɗaya daga cikin wannan ba. An ɓoye musu ma’anarsa, kuma ba su gane da abin da yake magana a kai ba.
Copyright information for
HauSRK