‏ Luke 18:35-43

Makaho mai bara ya sami ganin gari

(Mattiyu 20.17-19; Markus 10.32-34)

35Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara. 36Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa. 37Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.”

38Sai ya yi kira ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

39Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

40Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi ya ce, 41“Me kake so in yi maka?”

Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina so in sami ganin gari.”

42Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka; bangaskiyarka ta warkar da kai.” 43Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.
Copyright information for HauSRK