Luke 19:28-38
Shiga mai nasara
(Mattiyu 21.1-11; Markus 11.1-11; Yohanna 12.12-19)
28Bayan Yesu ya yi wannan magana, sai ya yi gaba zuwa Urushalima. 29Da ya kai kusa da Betfaji da Betani, a tudun da ake kira Dutsen Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, ya ce musu, 30“Ku je ƙauyen da yake gaba da ku. Da kuna shiga, za ku tarar da wani ɗan jaki, wadda ba wanda ya taɓa hawa, a daure a wurin. Ku kunce shi ku kawo nan. 31In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke kunce shi?’ Ku ce masa, ‘Ubangiji yana bukatarsa.’ ” 32Waɗanda aka aika su yi gaba suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya gaya musu. 33Suna cikin kunce ɗan jakin, sai masu ɗan jakin suka ce musu, “Don me kuke kunce shi?” 34Suka amsa suka ce, “Ubangiji ne na bukatarsa.” 35Suka kawo shi wurin Yesu. Suka sa rigunarsu a kan ɗan jakin, sa’an nan suka sa Yesu a kai. 36Yana cikin tafiya, sai mutane suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya. 37Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa, 38“Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”“Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!”
Copyright information for
HauSRK