‏ Luke 20:1-8

An yi shakkar ikon Yesu

(Mattiyu 21.23-27; Markus 11.27-33)

1Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa. 2Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?”

3Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini, 4baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?”

5Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 6Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.”

7Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.”

8Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”
Copyright information for HauSRK