‏ Luke 20:20-26

Biyan haraji ga Kaisar

(Mattiyu 22.15-22; Markus 12.13-17)

20Sai suka sa masa ido, suka aiki’yan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko. 21Sai’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. 22Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”

23Ya gane makircinsu, sai ya ce musu, 24“Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?”

Suka amsa, “Na Kaisar.”

25Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”

26Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru.
Copyright information for HauSRK