Luke 20:27-40
Ba aure a tashin matattu
(Mattiyu 22.23-33; Markus 12.18-27)
27Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa, 28“Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa’ya’ya.’ 29To, an yi waɗansu’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba’ya’ya. 30Na biyun, 31da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu’ya’ya. 32A ƙarshe, ita macen ma ta mutu. 33Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.” 34Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure, 35amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba. 36Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su’ya’yan Allah ne, tun da su’ya’yan tashin matattu ne. 37Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’ 38Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.” 39Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!” 40Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi.
Copyright information for
HauSRK