‏ Luke 20:41-44

Kiristi ɗan wane ne?

(Mattiyu 22.41-46; Markus 12.35-37)

41Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’ 42Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
“Zauna a hannun damana,
43 sai na sa abokan gābanka
su zama matashin sawunka.” ’
Zab 110.1

44 Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?”
Copyright information for HauSRK