Luke 20:9-19
Misalin’yan haya
(Mattiyu 21.33-46; Markus 12.1-12)
9Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya. 10A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin’ya’yan inabin. Amma’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi. 11Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi. 12Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje. 13 “Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’ 14 “Amma da’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’ 15Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi. “To, me mai gonar inabin zai yi da su? 16Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.” Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!” 17Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi,shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’ ▼
▼ Ko kuwa dutsen kusurwa
,
, ▼▼ Zab 118.22
18 Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.” 19Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane.
Copyright information for
HauSRK