‏ Luke 22:14-23

(Mattiyu 26.26-30; Markus 14.22-26; 1 Korintiyawa 11.23-25)

14Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa don cin abinci. 15Sai ya ce musu, “Na yi marmari ƙwarai don in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wahala. 16Ina dai gaya muku, ba zan ƙara cinsa ba, sai ya sami cika a mulkin Allah.”

17Bayan ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, sai ya ce, “Ku karɓa, ku rarraba wa junanku. 18Ina dai gaya muku, ba zan ƙara sha daga’ya’yan inabi ba, sai mulkin Allah ya zo.”

19Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”

20Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, “Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku. 21Amma hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni. 22Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka ƙaddara, amma kaiton mutumin da zai bashe shi.” 23Sai suka fara tambayar junansu, ko wane ne a cikinsu zai yi wannan.
Copyright information for HauSRK