Luke 22:39-46
Yesu ya yi addu’a a Dutsen Zaitun
(Mattiyu 26.36-46; Markus 14.32-42)
39Yesu ya fita zuwa Dutsen Zaitun kamar yadda ya saba, almajiransa kuma suka bi shi. 40Da ya kai wurin, sai ya ce musu, “Ku yi addu’a don kada ku fāɗi cikin jarraba.” 41Sai ya janye daga wurinsu, misalin nisan jifa, ya durƙusa a ƙasa ya yi addu’a, 42“Uba, in ka yarda, ka ɗauke mini wannan kwaf, amma ba nufina ba, sai dai naka.” 43Wani mala’ika daga sama ya bayyana gare shi, ya ƙarfafa shi. 44Domin tsananin azaba, sai ya ƙara himma cikin addu’a, zuffansa kuma na ɗigowa ƙasa kamar jini. 45Da ya tashi daga addu’a, ya koma inda almajiransa suke, sai ya iske su suna barci, daga gajiyar baƙin ciki. 46Ya tambaye su, “Don me kuke barci? Ku tashi ku yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba.”
Copyright information for
HauSRK