‏ Luke 22:55-57

55Amma da suka hura wuta a tsakiyar harabar gidan, kowa ya zauna, sai Bitrus ya zo ya zauna tare da su. 56Wata baiwa ta gan shi zaune kusa da wutar. Ta dube shi sosai sa’an nan, ta ce, “Ai, wannan mutum ma yana tare da shi.”

57Amma ya yi mūsu ya ce, “Mace, ban san shi ba!”
Copyright information for HauSRK