Luke 22:63-71
Masu gadi sun yi wa Yesu ba’a
(Mattiyu 26.59-66; Markus 14.55-64; Yohanna 18.19-24)
63Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa ba’a da dūka. 64Suka rufe masa idanu suna tambaya cewa, “Ka yi annabci! Wa ya mare ka?” 65Suka kuma yi masa waɗansu baƙaƙen maganganu masu yawa.Yesu a gaban Bilatus da Hiridus
66Da gari ya waye, sai majalisar dattawa na mutane, da manyan firistoci, da malaman dokoki, suka taru wuri ɗaya. Sai aka kawo Yesu a gabansu. 67Suka ce, “Ka faɗa mana, ko kai ne Kiristi?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ni ba, 68in kuma na yi muku tambaya ba za ku iya ba ni amsa ba. 69Amma daga yanzu, Ɗan Mutum zai zauna a hannun dama na Allah Mai Iko.” 70Sai dukansu suka yi tambaya suka ce, “Wato, kai Ɗan Allah ke nan?” Ya amsa ya ce, “Kun faɗa daidai, ni ne.” 71Sai suka ce, “Wace shaida kuma muke nema? Ai, mun ji abin da ya ce da bakinsa.”
Copyright information for
HauSRK