Luke 22:7-14
Abincin yamma na ƙarshe
(Mattiyu 26.17-25; Markus 14.12-21; Yohanna 13.21-30)
7Sai ranar Bikin Burodi Marar Yisti ta kewayo, wato, ranar hadayar ɗan ragon kafara na Bikin Ƙetarewa. 8Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna, ya ce musu, “Ku je ku yi shirye-shiryen Bikin Ƙetarewar da za mu ci.” 9Suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu je mu yi shirin?” 10Ya amsa ya ce, “Sa’ad da kuka shiga cikin gari, za ku sadu da wani mutum yana ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi zuwa gidan da zai shiga. 11Ku ce wa maigidan, Malam ya aike mu mu ce maka, ‘Ina ɗakin baƙi, inda ni da almajiraina za mu ci abincin Bikin Ƙetarewa?’ 12Zai nuna muku wani babban ɗakin sama a shirye. Nan za ku yi shirin.” 13Sai suka tafi, suka kuma iske kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.(Mattiyu 26.26-30; Markus 14.22-26; 1 Korintiyawa 11.23-25)
14Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa don cin abinci.
Copyright information for
HauSRK