Luke 23:13-26
(Mattiyu 27.15-26; Markus 15.6-15; Yohanna 18.39–19.16)
13Bilatus ya tara manyan firistoci, da masu mulki, da mutane, 14ya ce musu, “Kun kawo mini wannan mutum, a matsayin wanda yana zuga mutane su yi tawaye. Na bincike shi a gabanku, ban ga a kan me kuka kawo kararsa ba. 15Haka ma Hiridus, shi ya sa ya dawo da shi nan wurinmu. Kamar yadda ku ma kun gani, ba abin da mutumin nan ya yi, da ya isa mutuwa. 16Saboda haka, zan yi masa bulala, in sāke shi.” ▼▼Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da 17 A lokacin idi kuwa lalle ne ya sakar musu ɗaurarre guda.
17 ▼▼Wasu rubuce-rubucen ba su da rubutu a nan. Wasu suna da rubutu mai kama da Mat 27:15; Mrk 15:6.
– 18Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!” 19(Barabbas yana kurkuku saboda laifin tā da hankali a birnin, da kuma don kisankai.) 20Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu. 21Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” 22Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, sa’an nan in sāke shi.” 23Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi. 24Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu. 25Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda tā da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Sa’an nan ya ba da Yesu ga nufinsu. Gicciyewa
(Mattiyu 27.31-44; Markus 15.21-32; Yohanna 19.17-27)
26Sa’ad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya.
Copyright information for
HauSRK