Luke 4:1-13
Gwajin Yesu
(Mattiyu 4.1-11; Markus 1.12,13)
1Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada, 2inda kwana arba’in, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa. 3Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.” 4Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’ ▼▼M Sh 8.3
” 5Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya. 6Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama. 7Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.” 8Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’ ▼▼M Sh 6.13
” 9Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa. 10Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,su kiyaye ka da kyau;
11za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’ ▼
▼Zab 91.1,12
”12Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ▼
▼M Sh 6.16
” 13Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.
Copyright information for
HauSRK