Luke 4:16-30
(Mattiyu 13.53-58; Markus 6.1-6)
16Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majami’a kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yă yi karatu. 17Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta, 18 “Ruhun Ubangiji yana kaina,domin ya shafe ni,
in yi wa matalauta wa’azin bishara.
Ya aiko ni in yi shelar’yanci ga’yan kurkuku,
in kuma buɗe idanun makafi,
in ba da’yanci ga waɗanda aka danne.
19 In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.” ▼
▼ Ish 61.1 2
20Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa. 21Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.” 22Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?” 23Yesu ya ce musu, “Tabbatacce, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ” 24Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa. 25Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar. 26Duk da haka, ba a aiki Iliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon. 27Akwai kuma mutane da yawa a Isra’ila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Suriyan nan kaɗai.” 28Dukan mutanen da suke cikin majami’a suka fusata ƙwarai da jin wannan. 29Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa, 30amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa.
Copyright information for
HauSRK