‏ Luke 5:1-11

Kiran almajirai na farko

(Mattiyu 8.14-17; Markus 1.29-34)

1Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah, 2sai ya hangi jiragen ruwa biyu a bakin tafkin, waɗanda masu kamun kifi suka bari suna wankin abin kamun kifinsu. 3Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yă tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki.

4Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi.”

5Siman ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin.”

6Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har abin kamun kifinsu suka fara tsintsinkewa. 7Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa.

8Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!” 9Gama mamaki ya kama shi da abokansa duka, saboda yawan kifin da suka kama. 10Yaƙub da Yohanna,’ya’yan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki.

Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.”
11Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi.
Copyright information for HauSRK