‏ Luke 7:18-35

Yesu da Yohanna Mai Baftisma

(Mattiyu 11.1-19)

18Almajiran Yohanna suka gaya masa dukan waɗannan abubuwa. Sai ya kira biyu daga cikinsu, 19ya aike su wurin Ubangiji, su tambaya su ce, “Kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?”

20Da mutanen suka iso wurin Yesu, sai suka ce, “Yohanna Mai Baftisma ne ya aike mu wurinka, mu yi tambaya, ‘Ko kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?’ ”

21A daidai lokacin nan, Yesu ya warkar da mutane da yawa masu ciwo, masu cututtuka, da kuma masu mugayen ruhohi. Ya kuma ba makafi da yawa ganin gari. 22Sai ya amsa wa almajiran Yohanna ya ce, “Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka ji, da abin da kuka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin bishara. 23Mai albarka ne mutumin da bai yi shakkar bangaskiyar da yake da ita a kaina ba.”

24Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna ya ce, “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? 25In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da tufafi masu kyau ne? A’a, masu sa kayan tsada da suke cikin annashuwa, ai, a fada suke. 26Amma me kuka je kallo? Annabi? I, ina kuma faɗa muku, ya ma fi annabi. 27Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiko da ɗan saƙona yă sha gabanka,
wanda zai shirya hanya, a gabanka.’
Mal 3.1

28 Ina faɗa muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yohanna girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”

29(Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma. 30Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.)

31Yesu ya ci gaba da cewa, “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Kamar me suke? 32Suna kama da yaran da suke zama a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa, “ ‘Mun busa muku sarewa,
amma ba ku yi rawa ba,
Mun kuma yi muku waƙar makoki,
ba ku kuma yi kuka ba.’

33 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 34Ɗan Mutum ya zo yana ci, yana sha, sai kuka ce, ‘Ga mai yawan ci, mashayi, da kuma abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ 35Amma akan tabbatar da hikima ta gaskiya bisa ga dukan’ya’yanta.”
Copyright information for HauSRK