Luke 9:1-6
Yesu ya aiki sha biyun
(Mattiyu 10.5-15; Markus 6.7-13)
1Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka. 2Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya. 3Ya ce musu, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, wato, ba sanda, ba jaka, ba burodi, ba kuɗi, ba riga na biyu. 4Duk gidan da kuka sauka, ku zauna nan sai kun bar garin. 5In mutane ba su karɓe ku ba, sa’ad da kun bar garinsu, ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.” 6Sai suka tashi suka shiga ƙauye zuwa ƙauye suna wa’azin bishara, suna warkar da marasa lafiya a ko’ina.
Copyright information for
HauSRK