Luke 9:18-21
Shaidar Bitrus a kan Yesu
(Mattiyu 16.13-19; Markus 8.27-29)
18Wata rana sa’ad da Yesu yana addu’a a ɓoye, almajiransa kuma suna tare da shi, sai ya tambaye, su ya ce, “Wa, taron mutane ke ce da ni?” 19Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu kuma annabi Iliya, har wa yau waɗansu suna cewa, kai ɗaya daga cikin annabawan da ne, da ya tashi da rai.” 20 “Amma ku fa, wa, kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kiristi na Allah.”(Mattiyu 16.20-28; Markus 8.30–9.1)
21Yesu ya gargaɗe su da ƙarfi, kada su gaya wa kowa wannan magana.
Copyright information for
HauSRK