‏ Luke 9:28-36

Sāke kamanni

(Mattiyu 17.1-8; Markus 9.2-8)

28Bayan kamar kwana takwas da yin wannan magana, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yohanna, da kuma Yaƙub, suka hau kan dutse tare don yin addu’a. 29Yana cikin addu’a, sai kamannin fuskarsa ta sāke, tufafinsa kuma suka zama da haske kamar hasken walƙiya. 30Sai ga mutum biyu, Musa da Iliya, suka bayyana cikin kyakkyawar daraja, suna magana da Yesu. 31Suka yi zance a kan tashinsa, wanda shi ya kusan ya kawo ga cikarsa a Urushalima. 32Barci kuwa ya kama Bitrus da abokan tafiyarsa sosai. Da idanunsu suka warware, sai suka ga ɗaukakarsa da kuma mutum biyun tsaye tare da shi. 33Da mutanen na barin Yesu, sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, wato, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” (Bai ma san abin da yake faɗi ba.)

34Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije ya bayyana ya rufe su, sai suka ji tsoro, yayinda suke shiga cikin girgijen. 35Wata murya ta fito daga cikin girgijen, tana cewa, “Wannan Ɗana ne, zaɓaɓɓena, ku saurare shi.” 36Da muryar ta gama magana, sai suka tarar Yesu shi kaɗai ne. Almajiran kuwa suka riƙe wannan al’amari a zukatansu. A lokacin nan, ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.
Copyright information for HauSRK