Luke 9:37-43
Warkar da yaro mai mugun ruhu
(Mattiyu 17.14-18; Markus 9.14-27)
37Kashegari, sa’ad da Yesu tare da almajiran nan uku suka sauka daga kan dutsen, sai taro mai yawa ya haɗu da shi. 38Sai wani mutum daga cikin taron ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Malam, ina roƙonka, ka dubi ɗan nan nawa, gama shi ne kaɗai nake da shi. 39Wani ruhu yakan kama shi, sai ya yi ihu farar ɗaya. Yakan sa shi farfaɗiya, har bakinsa ya yi kumfa. Da ƙyar yake barinsa, yana kuwa kan hallakar da shi. 40Na roƙi almajiranka su fitar da shi, amma ba su iya ba.” 41Yesu ya amsa ya ce, “Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan.” 42Yaron yana kan zuwa ke nan, sai aljanin ya buga shi ƙasa, cikin farfaɗiya. Amma Yesu ya kwaɓe mugun ruhun, ya warkar da yaron, sai ya miƙa shi ga mahaifinsa. 43Duk suka yi mamakin girman Allah.(Mattiyu 17.22,23; Markus 9.30-32)
Yayinda kowa yana cikin mamakin dukan abubuwan da Yesu ya yi, sai ya ce wa almajiransa,
Copyright information for
HauSRK