‏ Mark 1:1-8

Yohanna Mai Baftisma ya shirya hanya

(Mattiyu 3.1-12; Luka 3.1-18; Yohanna 1.19-28)

1Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah.
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā ba su da Ɗan Allah.
2An rubuta a cikin littafin annabi Ishaya cewa, “Zan aika da ɗan aikena yă sha gabanka,
wanda zai shirya hanyarka,”
Mal 3.1

3“muryar mai kira a hamada tana cewa,
‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,
ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”
Ish 40.3

4Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. 5Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun. 6Yohanna ya sa tufafin gashin raƙumi, ya kuma yi ɗamara da fata. Abincinsa fāri ne da kuma zumar jeji. 7Wannan kuwa shi ne saƙonsa, “A bayana, wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban kuwa isa in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba. 8Ina muku baftisma da
Ko kuwa a cikin
ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”
Copyright information for HauSRK