‏ Mark 10:46-52

Bartimawus makaho ya sami gani

(Mattiyu 20.29-34; Luka 18.35-43)

46Sai suka iso Yeriko. Sa’ad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa (wato, “ɗan Timawus”), yana zaune a gefen hanya yana bara. 47Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, “Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

48Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yă yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

49Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kira shi.”

Sai suka kira makahon suka ce, “Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka.”
50Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu.

51Yesu ya tambaye shi ya ce, “Me kake so in yi maka?”

Makahon ya ce, “Rabbi, ina so in sami ganin gari.”

52Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.
Copyright information for HauSRK