‏ Mark 11:15-17

(Mattiyu 21.12-17; Luka 19.45-48; Yohanna 2.13-22)

15Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru, 16ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki. 17Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’?
Ish 56.7
Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon’yan fashi.’
Irm 7.11
Copyright information for HauSRK